Ramadan

Bah4...7SfM
13 Feb 2026
54

ℹ Dan Allah a daure a karanta har qarshe

JADAWALIN TSARE TSAREN YADDA ZAMU ANFANI WATAN RAMADAN
👇

1} _Kwacciya Bacci 10pm.
2} Tashi daga bacci 3am.
3} Sallar Dare 3:30am Zuwa 4:15am.
4} Karatun Al qur Ani Na Dakika 20 A kalla Ayoyi 10 tare da ma anar su. 4:15 - 4:35am. Ayi addu a ta Dakika 10, Rukar dukkanin Bukatu a wajan ubangiji 4:35 - 4:45.
5} Yin Sahur daga 4:45am Zuwa ketowar Alfijir.
6} Shirin Sallar Asubah Bayan Yin Sahur .
7} Sallar Asubah A kan lokacin ta.
8} Addu oin Safiya daga 6am/6:30am
9} Hutu Tare da shirye shiryan abubuwan da za a Gudanar a Ranar Har 7am.
10} Sallar Walaha, a kalla Raka a Hudu, Daga 9:00am zuwa 11:30am.
11} Yawaita Sauraran Karatun Al qur Ani.
12} Sallar Azahar A kan lokacin ta Tare da Addu oi a kalla na Dakika 10 zuwa 15.
13} Sallar La asar A kan lokacin ta Tare da Addu oi a kalla na Dakika 10 zuwa 15.
14} Shan Ruwa da Abinda Allah ya hure, Tare da yin addu oin dukkanin Bukatu a wajan ALLAH kafin Shan Ruwa da Kuma bayan ansha Ruwa, Hakika karbabbiya ce 
15} Sallar Isha I Tare da Nafila ta taraweeh har zuwa 9:00pm.
16} Bayan sallar taraweeh Sai ayi Nazarin yadda aka Tafiyar da Ranar Mutum Yayiwa Kansa wadannan Tambayoyi 
Me nayi Dai Dai ?
Me nayi ba dai dai ?
Wane Abu ya kamata na Daina ?
Wane Abu ya kamata na Fara ?.

   Bayan duk Wannan Sai a Dage Da Sadaka Ga Talakawa da mabukata.
 Ya Allah Ka nuna mana wannan Wata da Rai da Lafiya 

  Hanyar Sauke Al qur Ani a cikin kwana talatin 30
🕌 Asubah: Shafi 4
🕌 Azahar: Shafi 4
🕌 La asar: Shafi 4
🕌 Magariba: Shafi 4
🕌 Isha I : Shafi 4

  Hanyar Sauke Al qur Ani a cikin kwana Sha biyar 15 

🕌 Asubah: Shafi 8
🕌 Azahar: Shafi 8
🕌 La asar: Shafi 8 
🕌 Magariba: Shafi 8 
🕌 Isha i: Shafi 8.

Hanyar Sauke Al qur Ani a cikin kwana Sha biyar 15 

🕌 Asubah: Shafi 8
🕌 Azahar: Shafi 8
🕌 La asar: Shafi 8 
🕌 Magariba: Shafi 8 
🕌 Isha i: Shafi 8 

note
Ba dole bane se kabi wadanan hanyoyin Amma kayi iya yinka wajan tsananta ibada 
Allah ya bamu iko da Juriya💚

BULB: The Future of Social Media in Web3

Learn more

Enjoy this blog? Subscribe to AntiBara11

0 Comments