El-Rufa'i

5Khy...uy2c
14 Feb 2026
19

Wato kafin ka samu mutum mai irin salon Professor Isa Ali Pantami da wahala a cikin manyan kasar nan, duk yadda zaka soke shi, ka aibata shi, ka zage shi a fagen addini ko siyasa ba zai taba yi maka martani ba balle reply.

~ Kuma ba zai daina abinda yake yi ba, duk yadda kaso yayi magana ba zai yi ba, kuma duk maganar ka ba zata dakatar dashi ba, wannan ba abu ne me sauki ba, idan kana ganin abu ne me sauki ka gwada dauko wani abinda ya shafi rayuwar mutane kace zaka yi ka gani ko zaka iya yin hakuri akan wasu abubuwan da za'a fada maka.

Wannan abu ne da na koya a wajen sa, amma Ni kaina bana iya bin irin wannan salon nasa, dari bisa dari ince zanyi shiru akan komai, No, ba zai yiwu min ba. Da wahala ka samu wani mutum da Prof. Pantami ya zauna don yayi masa raddi a rubuce ko da baki saboda kawai ya soki matsayar sa.

Ka gama fadin duk abinda zaka fada akan sa, gobe da safe sai kaga ya cigaba da wannan abun da kai kake ganin ya tsaya maka a wuyan.

©Abdul-Hadee Isah Ibraheem

BULB: The Future of Social Media in Web3

Learn more

Enjoy this blog? Subscribe to MSY

0 Comments